London Escorts sunderland escorts
Friday, October 18, 2024

Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa yake tausayawa talakawa akan canjin kuɗi

Must read

Zamu Matse Enyimba Har Gida – Inji Aminu Bajahilci

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Aminu Sani yasha alwashin bawa marada kunya a wasan su na gaba da zasu fafata da...

Kisan Masu Maulidi: Gwamnati ba ta shirya yiwa musulmi adalci ba

Kisan Masu Maulidi: Gwamnati ba ta shirya yiwa musulmi adalci ba Ba mu gamsu da matakan da gwamnatin tarayya ta ce zata dauka don nuna...

Gwnanatin jahar kano ta bukaci malamai dasu cigaba da dafawa kokarin ta na wayar da Kan matasa Kan illolin shaye shaye a tsakanin alumma.

Gwnanatin jahar kano ta bukaci malamai dasu cigaba da dafawa kokarin ta na wayar da Kan matasa Kan illolin shaye shaye a tsakanin alumma. Gwnanan...

Maukibi: An ja hankalin mabiya darikar Qadiriyya da zasu fita Taron maukukibin Qadiriyya a gobe Asabar dasu zamo Masu da’a yayin fitowar ta su.

An ja hankalin mabiya darikar Qadiriyya da zasu fita Taron maukukibin Qadiriyya a gobe Asabar dasu zamo Masu da'a yayin fitowar ta su. Shekh Qaribullah...

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙasa a inuwar Jam’iyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce tushensa a matsayin ɗa ga ƴar kasuwa ne ya bashi damar fahimtar matsalar da canjin kudi ya kawowa a tsakanin al’umma.

Asiwajun cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai
Abdulaziz Abdulaziz ya fitar a ranar Asabar.

Tinubu, wanda a lokaci mabanbanta ya bayyana rashin dacewar sabon tsarin, ya ce a matsayinsa na wanda ya tashi a kasuwa, ya fahimci yadda yanayin zai yi ta’asiri a rayuwar masu ƙaramin ƙarfi.

A cewar sanarwar, da yake bayani a yammacin ranar Juma’a yayin wani taron ganawa da shugabannin yan kasuwa na ƙasa a Babban Birnin Tarayya Abuja, Ɗan Takarar na Jam’iyar APC ya ce mahaifiyar sa ta ciyar da shi da ilimantar da shi da kuɗin kasuwanci, ya kara da cewa yana iya fahimtar faduwa da riba na yan kasuwa.

Tinubu ya ce yana da masaniyar rashin zagawar wadatattun kuɗaɗe zai iya kawo tasgaro a tattalin arziki na yau da kullum.

Ya bayyana tausayawarsa ga ƙananun yan kasuwa tare da ƴan kasuwa da ke mu’amula da abubuwa masu saurin lalacewa, in da ya ce sune wɗanda tsarin zai fi shafa.

Tinubu ya bada misali da wani mai sayar da karas da ya hanga a yayin yawon neman zabe da ya tafi a Jahar Gombe, wanda ke tsaye kan kayansa a cikin rana ba tare kowa mai neman sayen kayan ba, yana mai cewa hakan ya faru ne saboda rashin kuɗi a hannun jama’a.

Dan takarar shugabancin ƙasar yayi kira ga ƴan kasuwa da kada su bari matsalar canjin kudin ya tunzura su.

Ya ce Idan har yayi nasarar lashe zabensa to zai kirkiri hanyar bayar da bashi mai sauƙi ga yan kasuwa tare da share musu dukkannin wata matsalar da ta addabe su a kasuwancinsu.

Tinubu ya bawa ƴan kasuwar tabbaci cewa ya san inda ke yi musu ƙaiƙayi kuma zai magance musu a matsayin sa na wanda ya fito daga gidan kasuwanci.

Wakilan shugabannin ƴan kasuwan da suka yi jawabi ga mahalarta taron sun bada kyakkyawar shaida a kan ɗan takarar wanda suka kira a matsayin daya daga cikin su.

Sunyi alkawarin bayar da ƙuri’u masu yawa domin nasarar Tinubu, wanda suka bayyana a matsayin wanda yafi sauran ƴan takarar nagarta.

Tinubu ya halarci Taron tare da Gwamnonin da suka hada da Muhammad Badaru Abubakar (na Jigawa) da Abubakar Sani Bello (na Niger), tare da sakataren majalisar yakin neman zabensa Hon. James Faleke, da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iya.

- Advertisement -

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

Latest article

Zamu Matse Enyimba Har Gida – Inji Aminu Bajahilci

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Aminu Sani yasha alwashin bawa marada kunya a wasan su na gaba da zasu fafata da...

Kisan Masu Maulidi: Gwamnati ba ta shirya yiwa musulmi adalci ba

Kisan Masu Maulidi: Gwamnati ba ta shirya yiwa musulmi adalci ba Ba mu gamsu da matakan da gwamnatin tarayya ta ce zata dauka don nuna...

Gwnanatin jahar kano ta bukaci malamai dasu cigaba da dafawa kokarin ta na wayar da Kan matasa Kan illolin shaye shaye a tsakanin alumma.

Gwnanatin jahar kano ta bukaci malamai dasu cigaba da dafawa kokarin ta na wayar da Kan matasa Kan illolin shaye shaye a tsakanin alumma. Gwnanan...

Maukibi: An ja hankalin mabiya darikar Qadiriyya da zasu fita Taron maukukibin Qadiriyya a gobe Asabar dasu zamo Masu da’a yayin fitowar ta su.

An ja hankalin mabiya darikar Qadiriyya da zasu fita Taron maukukibin Qadiriyya a gobe Asabar dasu zamo Masu da'a yayin fitowar ta su. Shekh Qaribullah...

Gwamnan jihar kano Abba kabir Yusuf ya jagoranci kaddamar da raba tikiti ga dalibai 1001 Wanda gwamnati ta dauki nauyin karo karatunsu na digiri...

Gwamnan jihar kano Abba kabir Yusuf ya jagoranci kaddamar da raba tikiti ga dalibai 1001 Wanda gwamnati ta dauki nauyin karo karatunsu na digiri...