Kisan Masu Maulidi: Gwamnati ba ta shirya yiwa musulmi adalci ba
Ba mu gamsu da matakan da gwamnatin tarayya ta ce zata dauka don nuna damuwarta da abun da sojoji suka yi na sakin bom akan mutanen dake Maulidi a garin Tudun biri dake karamar hukumar igabi a jihar Kaduna.
A cewar ambassador yusha’u yusif hamza falakin shinkafi
” Tunda abun nan ya faru duk abun da gwamnatin tayi da sunan alkawari ta yi shi wanda mu Muna ganin gaskiya ba lallai su iya cika alkawuran ba, da da gaske suke da yanzu an lalubo wadanda sukai abun an Kuma fara hukunta su, ba ayi ta yi mana alkawura ba”.
A Shekaru daban-daban sojoji sun kashe fararen hula da Bom A Arewacin Najeriya kamar haka:
1. Maris 16, 2014. Mutane 10 A Borno
2. Jan 17, 2017. Mutane 58 A Borno
3. Feb 28, 2018. Mutane 20 A Borno
4. Afrilu 11, 2019. Mutane 11 A Zamfara
5. Yuli 2, 2019. Mutane 13 A Borno
6. Afrilu 25, 2021. Mutane 30 A Borno
7. Sep 16, 2021. Mutane 9 A Yobe
8. Sep 26, 2021. Mutane 20 A Borno
9. Afrilu 20, 2022. Mutane 6 A Nijar
10. Yuli 6, 2022. Mutane 12 A Katsina
11. Dec 17, 2022. Mutane 60 A Zamfara
12. Jan 24, 2023. Mutane 18 A Nijar
13. Jan 25, 2023. Mutane 40 A Nasarawa
14. Maris 5, 2023. Mutane 3 A Kaduna
15. Aug 18, 2023. 1 Mutane A Nijar
16. Dec 3, 2023. Mutane 90+ A Kaduna.