An ja hankalin mabiya darikar Qadiriyya da zasu fita Taron maukukibin Qadiriyya a gobe Asabar dasu zamo Masu da’a yayin fitowar ta su.
Shekh Qaribullah Shekh Nasir kabara Kuma shugaban darikar Qadiriyya na Afrika, shine yai wannan kiran a yayin fara tarukan maukibin na bana Wanda zai kasance karo na 73.
Shekh Qaribullah kabara ya Kuma Yi kira ga mabiya darikar dasu kauracewa fita da janarato dake Amfani da tukunyar iskar gas, domin kaucewa afkuwar gobara, haka Kuma yaja kunnen Masu fita da shigar da Bata kamata ba, kokuma askin da Bai kamata ba.
Akarshe malamin yayi fatan za ayi Taron maukukibin na bana Lafiya akuma gama Lafiya.