Gwnanatin jahar kano ta bukaci malamai dasu cigaba da dafawa kokarin ta na wayar da Kan matasa Kan illolin shaye shaye a tsakanin alumma.
Gwnanan Kano Alhaji Abba Kabir yusif ne ya bayyana hakan yau yayin bikin maukibin kadiryya karo na sabain da Uku Wanda ya gudana a masallacin kanzu dake Kan titin hanyar zuwa Katsina.
Gwamna Abba Kabir Wanda Mataimakin sa kwamared Aminu Abdussalam gwarzo ya wakilta yace yaki da Shan miyagun kwayoyi tsakanin matasa ba abune me wahalaba ga gwamnatin in har malamai zasu dafa da addu’oi da wayar da Kan matasa ,ya Kuma bukaci gidajen dariku da izala dasu dafawa tsare tsaren gwamnati na auren zawarawa da makarantar ilimin qurani da aka Samar tare da sanya alummar musulmi dake kasar galasdinu cikin addu’a domin Samin sauki halin da suke ciki.
A jawabinsa Shugaban darikar kadiryya na Africa shiekh kariballa shiekh Nasiru Kabara ya bukaci Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da gwamnan Kano dasu Yi kokari waje sauke nauyin daya rataya akansu na Samar da tsaro duba da yadda wasu daga cikin makwabtan jahar nan ke fama da rashin tsaro.
Ya Kuma bukacesu dasu Samar da wasu hanyoyi da alumma zasu sami sauki rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya tayi.
Wakilin mu Kassim Gambo Kassim ya rawaito Mana cewa Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya Sami wakilcin karamin ministan gidaje Tijjani Muhammad gwarzo da wakilin sarkin musulmi tare da wakilin sarkin Kano tare da manyan malamai daga kasashen ketare da jihohim kasarnan.