Gwamnan jihar kano Abba kabir Yusuf ya jagoranci kaddamar da raba tikiti ga dalibai 1001 Wanda gwamnati ta dauki nauyin karo karatunsu na digiri na biyu a jami’o’in cikin gida Dana ketare.
Gwamnan yace tayi duba batare da siyasa ba wajen tantance wadannan dalibai ta kuma kashe kimanin kudi Naira biliyan hudu da miliyan Dari shida
Yace daliban za su fara tashi a gobe Jumaa afilin tashin jirgin sama na malam Aminu kano India ya bukace su dasu zamo jakadu na gari
Daga bisani yace anfara wannan shiri tun alokacin gwamnatin Injiniya Rabiu Musa kwankwaso
Dayake nasa jawabin tsohon gwamnan jihar kano Injiniya Rabiu musa kwankwaso ya godewa Allah da yanuna masa wannan rana ya kuma bukaci daliban dasu kula da addininsu da dabiunsu na gari.
Shima a nasa jawabin kwamishin ilimi mai Zurfi na jihar kano Dr Yusuf Ibrahim kofar mata ya godewa gwamnati da namijin kokarin data yi na cigaba da wannan shiri
wakilimmu Murtala Abdullahi baba ya rawaito mana cewa Sarkin kano Alh Aminu Ado bayero amadadadin sarakunan jihar ya bayyana farin cikinsa ya kuma bukaci daliban dasu zamo jakadu na gari