ANYI KIRA DA GOBNATIN TARAYYA DATA BUDE IYAKOKIN MAIGATARI, MAI ADUWA, KWANGWALAN DATA ILELA
Dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Dala kuma mataimakin Shugaban marasa rinjaye azauran majalisar wakilai ta kasa Hon. Aliyu Sani Madakingini Ya gabatar da wannan kuduri jiya Talata a zaman majalisar. Dan majalisar yakara da cewa wadannan Iyakoki wanda suka da Maigari a jahar Jigawa. Mai Aduwa da kwangwalan a jahar Katsina da kuma Ilela a jahar Sokoto. Duk da jahar Kano na zama babbar cibiyar kasuwancin kasa da kasa wanda ake gudanarwa tsakanin ‘yan kasuwar Najeriya da ‘yan kasuwar dasuka fito daga makotan kasarnan kamar kasar Nijar, Mali, Chadi, Kamaru, sauran kasashen dasuka hada Iyaka da Najeriya.
Aliyu Madaki yace duk da munasane da takunkumin da Majalisar kula da Raya Tattalin Arziqin Kasashen Yammacin Afirka tasakawa Sojojin dasuyi juyin mulki a kasar Nijar.
Haka zalika, Madakin Gini yakara da cewa ta dalilin rufe Iyakokin yajawo takaitar zirga zirgar Al’umomin dake Iyakokin. Kuma yakawo yankewar huldar kasuwancin dayake gudana tsawon shekaru, musamman ma jahar Kano wadda tazama cibiyayar kasuwancin Arewacin Najeriya.
Dan majalisar yakara da cewa, rufe Iyakokin yahaifar da yawaitar Fasa Kauri kuma yajawo karuwar shigar matasa aiyukan Ta’addanci wanda yakawo rashin tsaro a jahohin dake Arewacin Najeriya.
Akarshe Aliyu Madakin Gini Yace Idan Gobnatin Tarayya tasake bude wadannan Iyakokin sannan akasa matakan tsaro sosai ga dukkan kayan da za’a shigo dasu kasarnan hakan zai haifar da cigaban zaman lafiya da kyakykyawar alakar dake tsakanin Najeriya da kasashe makotan. Kuma zai magance yawaitar Fasa Kauri wanda hakan yana kawo nakasu ga Tattalin Arziqin Najeriya.