Wednesday, November 6, 2024

Dankwambo ya bukaci Inuwa ya daina kamfe muddin ya iya barazana

Must read

Zamu Matse Enyimba Har Gida – Inji Aminu Bajahilci

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Aminu Sani yasha alwashin bawa marada kunya a wasan su na gaba da zasu fafata da...

Kisan Masu Maulidi: Gwamnati ba ta shirya yiwa musulmi adalci ba

Kisan Masu Maulidi: Gwamnati ba ta shirya yiwa musulmi adalci ba Ba mu gamsu da matakan da gwamnatin tarayya ta ce zata dauka don nuna...

Gwnanatin jahar kano ta bukaci malamai dasu cigaba da dafawa kokarin ta na wayar da Kan matasa Kan illolin shaye shaye a tsakanin alumma.

Gwnanatin jahar kano ta bukaci malamai dasu cigaba da dafawa kokarin ta na wayar da Kan matasa Kan illolin shaye shaye a tsakanin alumma. Gwnanan...

Maukibi: An ja hankalin mabiya darikar Qadiriyya da zasu fita Taron maukukibin Qadiriyya a gobe Asabar dasu zamo Masu da’a yayin fitowar ta su.

An ja hankalin mabiya darikar Qadiriyya da zasu fita Taron maukukibin Qadiriyya a gobe Asabar dasu zamo Masu da'a yayin fitowar ta su. Shekh Qaribullah...

Tsohon gwamnan jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo ya bukaci Gwamnan jihar ta Gombe Muhammad Inuwa Yahaya da ya daina kamfe muddin ya iya wa mutane barazana.

Dankwambo ya bayyana hakanne a yankin Suwa na karamar hukumar Balanga da ke kudncin jihar lokacin yakin neman zabe na dan takarar gwamnan jiha a Jam’iyar PDP, Muhammad Jibrin Barde.

Ibrahim Dankwambo ya yi zargin cewar jam’iyar APC na yi wa mutanen jihar barazana a yakin neman zabe da ta ke yi.

Ibrahim Dankwambo wanda ya bayyana cewar an tafka kuskure wajen zabin jam’iyar APC  a zabe da ya gabata, ya bukaci masu zabe a yankin da ka da su sake kuskuren zaben APC.

Dankwambo ya kara da cewar duk wanda bai ji a jikinsa ba a yanzu ya ji da kunnensa irin halin da a ka jefa jama’a a ciki.

A jawabinsa dan takarar gwamnan jihar a PDP Muhammad Jibrin Barde ya yi kira wa mutanen yankin da su tabbatar sun zabi yan takarar jam’iyar PDP a dukkan matakai a zabe da ke tafe.

Ya kuma yi al’kawarin daukan matakai da su ka dace wajen bunkasa harkar noma a yankin, ya na mai cewar zai tabbatar da bude madatsar ruwa ta Balanga a kwanaki 100 na farkon mulkinsa.

- Advertisement -

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

Latest article

Zamu Matse Enyimba Har Gida – Inji Aminu Bajahilci

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Aminu Sani yasha alwashin bawa marada kunya a wasan su na gaba da zasu fafata da...

Kisan Masu Maulidi: Gwamnati ba ta shirya yiwa musulmi adalci ba

Kisan Masu Maulidi: Gwamnati ba ta shirya yiwa musulmi adalci ba Ba mu gamsu da matakan da gwamnatin tarayya ta ce zata dauka don nuna...

Gwnanatin jahar kano ta bukaci malamai dasu cigaba da dafawa kokarin ta na wayar da Kan matasa Kan illolin shaye shaye a tsakanin alumma.

Gwnanatin jahar kano ta bukaci malamai dasu cigaba da dafawa kokarin ta na wayar da Kan matasa Kan illolin shaye shaye a tsakanin alumma. Gwnanan...

Maukibi: An ja hankalin mabiya darikar Qadiriyya da zasu fita Taron maukukibin Qadiriyya a gobe Asabar dasu zamo Masu da’a yayin fitowar ta su.

An ja hankalin mabiya darikar Qadiriyya da zasu fita Taron maukukibin Qadiriyya a gobe Asabar dasu zamo Masu da'a yayin fitowar ta su. Shekh Qaribullah...

Gwamnan jihar kano Abba kabir Yusuf ya jagoranci kaddamar da raba tikiti ga dalibai 1001 Wanda gwamnati ta dauki nauyin karo karatunsu na digiri...