Gwamnatin jihar kano ta bukaci tubabbun yan dabar da suka ajiye makamansu da suzo a hada kai dasu don kara Samar da zaman lafiya a jihar kano.
Gwamna Abba kabir Yusuf ne ya bayyana haka alokacin da yayi taron taya tubabbun murnar zama jakadu na gari a rufaffen dakin taro dake satadiyon din sani Abacha kofar mata.
Gwamnan ya kara da cewa ashirye gwamnati take ta dauki nauyin dukkan Wanda zai koma makaranta tun daga matakin firamare har zuwa jami’a.
Ya kuma bayyana cewa nan da mako biyu zaayi bikin basu tallafi da kuma koya masu Sana’oin dogaro da kai
daga bisani ya yabawa kwamishinan yan sanda na jihar kano Muhd Usaini Gumel.
Da yake nasa jawabin kwamishinan yansanda na jihar kano yayi kira ga malamai da alumma dasu cigaba dayi musu addua da kuma jansu ajiki batare da nuna masu banbanci ba
Wakilimmu Murtala Abdullahi Baba ya rawaito mana cewa sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero ya yabawa da gwamnatin jihar kano da kwamishinan yansanda bisa yadda sukayi tunanin hada kai da tubabbun wajen Samar da zaman lafiya a jihar kano ya kuma bukaci alumma da acigaba da addua don samun dorewar zaman lafiya a jihar.