Zababbaun yan wasan kungitar kwallon kafa ta kano selected da suka fafata a gasar cin kafin Ahlan Ahlan Pre season ta 2023 sun chanchanci yabo tare da fidda mara ‘Da kunya inji jahoran kungiyar kuma shugaban kungiyar A K Boys Alhaji Muktar Magaji Ismail (a.k.a Alhaji Muktar Awarwasa fc )
A tattaunawa ta musamman da wakilinmu Chairman Alhaji Muktari .yace gasar Ahlan ta bana ta bada dama ga matasan yan wasan jihar kano damar bajekolin basirar su a fagen wasan kwallon kafa a fadin jihar nan
Matashin shugaban kungiyar AK Boys wanda a karon farko ya jagoranci zababbun yan wasan jihar kano ya kara da cewa yan wasa da dama sun sami kungiyoyi da yabo a lokacin wannan gasa inda yace hakan wata alamace da take nuna irin yadda yan waaan da sabuwar kungiyar suka karbu a idon jama’a
Da yake amsa tambaya kan abin dayafi daukkar hankali a gasar ta bana sai yace ” a gaskiya masu koyar da wasan saboda jajircewar su duk da cewa ba wani kudi ake basu ba, haka kuma suma yan wasan jihar kano sunyi abin a yaba kwarai ” inda yace yan wasan sun taka rawar gani inda suka gama da maki 7 a rukuni,
Dan gane da yadda aka hada yan wasan kungiyar Alhaji Mutari awarwasa cewa yayi masu horarwa sunyi kokari wajen zabin yan wasan ba tare da sanrai ko san zuciyaba ” a gaskiya na yabawa masu horarwar ”
Dangane da makomar kungiyar kasancewarta kungiya data burge alumma Alhaji Mutari kira yayi ga masu hannu da shuni dasu kalli kungiyar kuma su zuba jari a cikinta hakan zai taimakawa yan wasan da cigaban Makano,
Dangane da yadda yan wasan jihar kano suke, Matashi Shugaban kungiyar AK Boys din cewa yayi ” a gaskiya sai yaran jihar kano sun chanja hali na yadda zasu yadda wasan kwallon kafa sana’a ce mai kyakykyawar makoma,
Alhaji Muktari ya kara da godewa duk masu ruwa da tsaki a harkar wasan kwallon kafa a jihar kano musamman shugaban hukumar kwallon kafa ta jiha Sharu Rabiu Ahlan bisa yadda suka bashi goyon baya da karfafa gwiywa a lokacin da yake jagorantar kungiyar,