Friday, February 3, 2023
Home Wasanni An fidda Jadawalin Gasar Cin Kofin Manjo Janar Sunday Igbinowanhia Karo na...

An fidda Jadawalin Gasar Cin Kofin Manjo Janar Sunday Igbinowanhia Karo na Goma a Jihar Kano,

Gasar Cin Kofin Major Janar Sunday Igbinowanhia Ta Shiga Shekara ta Gkin fidda jadawalin gasar cin kofin major general sunday igbinowanhia karo na goma ya zama abin kallo da kwaykwayo ga masu shirya gasa makamanciyar ta a jihar kano, laakari da yadda aka tsara taron fidda jadawali na kakar wasan bana a babban hotel din ” Chilla ” dake jihar kano,

Taron daya samu wakilcin manyan jamian sojoji dake rike da Bokavu da Airforce base ya zama abin shaawa da alfahari ga masu shirya gasar musamman yadda aka tsara dakin taron da kowa yayi murna dashi,

Wani abin kari shaawa da armashi shine yadda manya jamian kula da wasan kwallon kafa na jihar kano suka albarkaci taron da yadda yan jaridu da marubuta labarin wasanni suka yiwa taron tsinke tare da kwarmata taro tunda sanyin safiya abinda ya sanya daukar hankalin maabota harkokin wasan kwallon kafa a jihar

Kungiyoyi 30 aka raba zuwa rukuni shida bayan fidda manyan kungiyoyi da suka taba lashe gasar ko sukayi fice a cikin ta, kungiyoyi irinsu Jogana United, Arab site, Norway Academy da wasaunsu na daga cikin wadanda aka baiwa rukunin kaitsaye saboda irin rawar da suka taka cikin gasar,

Injiniya Mato Haladu Jogana shine shugaban kwamitin shirya gasar ya bayyan irin kokari da Major Janar Sunday keyi da cewa abin ayabane laakari da yadda yake dawainiya da gasar shekaru 10 ba tsayawa,

Mato ya kara da cewa irin ayyukan kyautatawa alumma maza da mata da matasa da major janar keyi ga yan asalin jogana da jihar kano abune da ba kowa ke iya yiba,DA ga an sai ya godewa Manjo Jabar Sunday bisa abubuwan kyautatawa da soyayya da  yake yiwa alummar sa na Jogana ,Gezawa da Alummar jihar kano baki daya,

 

RELATED ARTICLES

Yan Wasan Kungiyar Kano Selected Sun Chanchanci Yabo – Alhaji Mutari Awarwasa

Zababbaun yan wasan kungitar kwallon kafa ta kano selected da suka fafata a gasar cin kafin Ahlan Ahlan Pre season ta 2023 sun chanchanci...

Christiano Ya Zura Kwallaye Biyu a Wasan da PSG ta Lallasa Riyadh All Stars

Cristiano Ronaldo ya ci kwallaye biyu a lokacin da Messi ta PSG ta doke Riyaad tauraruwarsa a bugun daga kai sai mai tsaron gida Kwallaye...

Hattara da Yan Wasa Biyu Na Arsenal Sunada Hatsari – Evra Ya Ya Gargadi Yan Manchester United

Tsohon dan wasan baya na Manchester United Patrice Evra, ya gargadi 'yan wasan kungiyar da su yi taka-tsan-tsan game da barazanar harin da Arsenal...

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Yan Wasan Kungiyar Kano Selected Sun Chanchanci Yabo – Alhaji Mutari Awarwasa

Zababbaun yan wasan kungitar kwallon kafa ta kano selected da suka fafata a gasar cin kafin Ahlan Ahlan Pre season ta 2023 sun chanchanci...

An fidda Jadawalin Gasar Cin Kofin Manjo Janar Sunday Igbinowanhia Karo na Goma a Jihar Kano,

Gasar Cin Kofin Major Janar Sunday Igbinowanhia Ta Shiga Shekara ta Gkin fidda jadawalin gasar cin kofin major general sunday igbinowanhia karo na goma...

Kwanaki Kadan Bayan Raba Gari da Tafiyar Bola Tinubu, Hajiya Najaatu ta Ziyarci Atiku Abubakar Har Gida

Fitacciyar ‘yar fafutuka kuma ‘yar siyasar Kano, Hajiya Naja’atu Mohammed, ta cika sa’o’i 72 da ficewa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tare da...

Christiano Ya Zura Kwallaye Biyu a Wasan da PSG ta Lallasa Riyadh All Stars

Cristiano Ronaldo ya ci kwallaye biyu a lokacin da Messi ta PSG ta doke Riyaad tauraruwarsa a bugun daga kai sai mai tsaron gida Kwallaye...

Recent Comments