Friday, February 3, 2023
Home Labarai Labaran Express Sabuwar Shekara: Dala miliyan 6.5 aka kashe wajan dinka rigar da aka...

Sabuwar Shekara: Dala miliyan 6.5 aka kashe wajan dinka rigar da aka sauyawa Ka’aba.

An sauyawa dakin Kaaba sabuwar riga wato Kiswah, da aka kashe dala miliyan 6.5 wajen ɗinkata a safiyar wannan Asabar din.

An soma aikin sauya rigar tun daren Juma’a bayan Sallar Isha’i aka zuwa asubahin Asabar, wanda ya zo daidai da ranar 1 ga watan Muharram 1444 A.H.

An kiyasata cewa nauyin sabuwar rigar ya kai kilogram 850, kuma a yanzu ya kasance irin wannan riga mafi tsada a duniya.

Wannan shi ne karon farko da ake sauya Kiswah wato kamar yada ake kiran rigar, a ranar 1 ga watan Muharram.

Kafin wannan lokaci ana sauyawa Kaaba rigar ne a lokacin aikin Hajji, musamman a safiyar 9 ga watan Dhul Hijjah idan alhazai sun tafi hawan Arafa.

Karkashin jagorancin Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais da ke kula da manyan masallatai biyu mafi daraja a duniya, ya ce an sauya lokacin sauya rigar Kaaba ne bisa sabbin dokoki da shawarwari masarautar Saudiyya.

Mutane sama da 200 ne dai kafofin yada labarai ke cewa suka yi aiki akan rigar Kaaba daga wajen dinkata har zuwa ta sanyata a jikin Kaaba.

RELATED ARTICLES

Mun kafa kungiyar da zatai mana aikin da zamuci zabe-Murtala Sule Garo

Tsohon kwamishinan kananan hukumomin kuma Dan takarar mataimakin Gwamnan Kano a Jam'iyyar APC Hon. Murtala Sule Garo ya kaddamar da Shugabanin kungiyar Gawuna Garo...

Rushewar gini-Wani Dalibin sakandire ya rasa ransa a kano sakamakon ginin makarantarsu daya fado masa

Wani dalibi Mai Suna mustapha salisu ya rasa ransa a safiyar wanan Rana biya bayan ginin wasu ajujuwa da ba'a kammalaba da suka rifto...

Za’a fara kama duk mashin din da baida rijista a Najeriya-Road Safety

Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa, FRSC, ta umarci kwamandojin sassan 37 na faɗin ƙasar nan da su kama duk wani babur mai kafa biyu...

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Yan Wasan Kungiyar Kano Selected Sun Chanchanci Yabo – Alhaji Mutari Awarwasa

Zababbaun yan wasan kungitar kwallon kafa ta kano selected da suka fafata a gasar cin kafin Ahlan Ahlan Pre season ta 2023 sun chanchanci...

An fidda Jadawalin Gasar Cin Kofin Manjo Janar Sunday Igbinowanhia Karo na Goma a Jihar Kano,

Gasar Cin Kofin Major Janar Sunday Igbinowanhia Ta Shiga Shekara ta Gkin fidda jadawalin gasar cin kofin major general sunday igbinowanhia karo na goma...

Kwanaki Kadan Bayan Raba Gari da Tafiyar Bola Tinubu, Hajiya Najaatu ta Ziyarci Atiku Abubakar Har Gida

Fitacciyar ‘yar fafutuka kuma ‘yar siyasar Kano, Hajiya Naja’atu Mohammed, ta cika sa’o’i 72 da ficewa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tare da...

Christiano Ya Zura Kwallaye Biyu a Wasan da PSG ta Lallasa Riyadh All Stars

Cristiano Ronaldo ya ci kwallaye biyu a lokacin da Messi ta PSG ta doke Riyaad tauraruwarsa a bugun daga kai sai mai tsaron gida Kwallaye...

Recent Comments