Sunday, November 27, 2022
Home RAHOTO Bayan mamayar Rasha ga Ukraine, Koriya ta harba makami mai linzami akalla...

Bayan mamayar Rasha ga Ukraine, Koriya ta harba makami mai linzami akalla guda daya, a matsayin gwaji

Hafsan hafsoshin sojojin Koriya ta Kudu sun sanar da cewa, Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami da ke gabashin gabar tekun Koriya a ranar Lahadi.

An harba makamin daga yankin Sunan na Koriya ta Arewa da misalin karfe 7.52 na safe agogon kasar, in ji rundunar hadin gwiwa.

Ministan tsaron Japan Nobuo Kishi ya ce Koriya ta Arewa ta harba “aƙalla makami mai linzami guda ɗaya”, wanda ya yi tafiya mai nisan kilomita 300 (mil 186) kuma ya kai tsayin kilomita 600 (mil 373), in ji CNN.

Kwamitin tsaron kasar Koriya ta Kudu (NSC) ya ce harba makamin ba abu ne da ake so ba don tabbatar da zaman lafiya yayin da duniya ke kokarin warware yakin Ukraine, a cewar fadar Blue House, ofishin shugaban kasar Koriya ta Kudu.

NSC ta kuma nuna matukar damuwa da nadama matuka dangane da harba makami mai linzami karo na takwas a bana, sannan ta bukaci Arewa da ta gaggauta dakatar da ayyukan da suka sabawa sulhu ta hanyar diflomasiyya.

Koriya ta Arewa ta kara kaimi wajen gwajin makami mai linzami a shekarar 2022, inda ta sanar da shirin karfafa garkuwarta”. a cewar kafofin yada labaran kasar.

DAILY TRUE HAUSA ta ruwaito cewa A cikin makonni hudun farko na shekarar 2022 kadai, Koriya ta Arewa ta kaddamar da gwaje-gwajen harba makami mai linzami guda bakwai, amma babu daya daga cikin makamanta masu cin dogon zango.

Manazarta sun ce karin gwajin da aka yi a bana ya nuna cewa Kim yana kokarin cimma burin cikin gida da kuma nuna wa duniya da ke kara tabarbarewa cewa Pyongyang karanta yakai tsaiko

“Pyongyang tana da kyakkyawan tsari na soji. Karfin gwamnatin Kim da sahihancinsa na da nasaba da gwada harba makamai masu linzami.”

RELATED ARTICLES

NDLEA operatives arrest 2 Pakistani businessmen with cocaine concealed in PA system

Two Pakistani businessmen were on Saturday, November 5, 2022 arrested with 8 kilograms of cocaine concealed in a Public Address (PA) system while attempting...

Takarar Shugaban Kasa A 2023: Jerin Manyan Jigajigan Jamiyyar APC 4 Da Ake Saran Shugaba Buhari Zai Amince A Matsayin Magajinsa

‘Yan Najeriya za su zabi sabon Shugaban kasa nan da watanni 11. A yayin da ake kara zafafa fafatawa a zaben shugaban kasa...

Bayani Sanya Hannu Kan Kudirin Dokar Zabe Da Aka Yiwa Gyara Da Shugaba Buhari Ya Yi

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu akan kudirin dokar zabe da aka yiwa gyara kuma ya zama doka. Shugaban Kasar ya sanya hannu akan...

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

NDLEA operatives arrest 2 Pakistani businessmen with cocaine concealed in PA system

Two Pakistani businessmen were on Saturday, November 5, 2022 arrested with 8 kilograms of cocaine concealed in a Public Address (PA) system while attempting...

Kotu- wani matashi Hukuncin kwashe kwata

Wata kotun shari'ar muslunci dake Zamanta a rijiyar lemo karkashin Mai shari'a Abdu Abdullahi wayya, ta yakewa wani matashi Mai suna Munzali Lawan, mazaunin...

Lemmy.Adede Ya Zama Gwarzo Mai Horarwa A Gasar Ahlan ta Rijiyar Zaki

Matashin mai horar da wasan kwallon kafa da ya ja kungiyar Ramcy dake gidan sarki a birnin kano Bashir Isyaku Yakasai wanda akafi sani...

Mun kafa kungiyar da zatai mana aikin da zamuci zabe-Murtala Sule Garo

Tsohon kwamishinan kananan hukumomin kuma Dan takarar mataimakin Gwamnan Kano a Jam'iyyar APC Hon. Murtala Sule Garo ya kaddamar da Shugabanin kungiyar Gawuna Garo...

Recent Comments